Psychology na Kasuwanci (Trading Psychology)
Ilimin halayyar ɗan adam yana da matuƙar mahimmanci don samun nasara a harkar kasuwanci. Wadannan shawarwari guda biyar zasu taimaka maka wajen sarrafa motsin zuciyarka yayin kasuwanci:
Don Maganin Kwadayi:
Kuyi biyayya ga dokokin ku, wato tsarin kasuwancin ku (Trading plan) da kuka tsara wa kanku tun farko. Kada ku bari kwadayi ya rinjaye ku.
Don Maganin Tsoro:
Dole ku kasance a shirye don fuskantar asara. Tunanin cewa zaku iya yin asara kafin ku fara kasuwanci zai taimaka muku rage tsoro da kuma yanke shawara da kyau.
Don Maganin Damuwa:
Ku kula da sarrafa haɗari (Risk Management). Rage haɗarin da ke akwai zai taimaka muku kare asusun kasuwancin ku, kuma hakan zai rage damuwa.
Don Maganin Fushi Bayan Asara:
Idan kun yi asara, kada ku bari fushi ya rinjaye ku. Ku maida hankali kan damar da ke gaba, kuma kuyi imani cewa za ku yi nasara.
Kafin Fara Kasuwanci:
Kada ku yi amfani da kuɗin da idan kun yi asarar su za su ba ku damuwa. Yin amfani da kuɗin da za ku iya sadaukarwa zai taimaka muku kasuwanci cikin kwanciyar hankali.
Karin Shawara:
Idan ka bari motsin zuciyarka ya rinjaye ka yayin kasuwanci, asara za ta iya shiga. Kada ka damu da abin da za ka iya rasa, kuma ka ɗauke shi kamar kuɗin da ba nawa ba ne (wato wanda za ka iya sadaukarwa). Wannan tunanin zai taimaka maka wajen samun riba mai yawa.





