Ma'anar Trade Na Cyptocurrency






Fahimtar Cryptocurrency: Mene Ne da Yadda Yake Aiki?

Cryptocurrency wani nau'in kuɗi ne na dijital da ake amfani da shi wajen ciniki da hada-hadar kuɗi, amma baya ƙarƙashin ikon wata gwamnati ko wata cibiyar kuɗi. Ya bambanta da kuɗin banki wanda ke ƙarƙashin kula da tsarin gwamnatin ƙasa. Kalmar nan ta "Crypto" tana nufin "ɓoyayye" ko "mai sirri", yayin da "Currency" kuma na nufin "kuɗin da aka amince da shi." Idan aka haɗa su wuri ɗaya, "Cryptocurrency" na iya nufin "Kuɗin da aka ɓoye" wanda ke nuna cewa ba a ganin su a zahiri, amma ana iya ganin bayanan su a rubuce (misali, lambobi).


Dalilin Kirkirar Cryptocurrency da Amfaninsa

An ƙirƙiro Cryptocurrency ne don ciniki ta yanar gizo. Ya shahara musamman a tsakanin kamfanoni da kuma mutane saboda ba shi da iyaka wajen tura kuɗi. Mutum zai iya tura wa abokin kasuwancinsa ko nawa ne ba tare da gwamnati ta san da wannan cinikin ba. Saboda wannan sirri da yake bayarwa, mutanen da ke amfani da shi sun haɗa da masu yin manyan hada-hadar da suka dace da doka har ma da waɗanda ba su dace ba.

Haka kuma, mutane da yawa suna samun kuɗi ta hanyar yin ciniki (trading) da shi. Saboda darajar cryptocurrency na hawa da sauka a kowane lokaci, masu ciniki suna siyan tsabar kuɗi (coins) a lokacin da darajarsu ta yi ƙasa, idan kuma ta haura sai su sayar don samun riba.


Alakar Cryptocurrency da Banki

Wasu ƙasashe sun amince da amfani da cryptocurrency, yayin da wasu kuma ba su amince da shi ba, kuma kowace ƙasa na da dalilinta na kin amincewa. Amma duk da haka, ana iya haɗa kuɗin banki da na cryptocurrency.

Hanyar P2P (Peer-to-Peer) A ƙasashen da ba su amince da cryptocurrency ba, mutane suna amfani da hanyar P2P don siye da siyarwa ba tare da banki ya gane ba. Misali, za ka iya tura wa wani kuɗi ta banki, sannan ya turo maka da cryptocurrency a asusunka. Amma idan ka yi amfani da katin bankinka (card) wajen siyan cryptocurrency kai tsaye, to bankin zai iya gane inda kuɗinka suka je.


Bitcoin: Uban Cryptocurrencies

Bitcoin shine cryptocurrency na farko kuma shine mafi girma a duniya. Idan har kana son kirkirar wani sabon cryptocurrency, dole ne ya dogara ne akan Bitcoin.

  • Kirkirar Bitcoin: An kirkiri Bitcoin a shekarar 2008 ta wani mai suna Satoshi Nakamoto. Ya boye ainihinsa, kuma tun daga wancan lokacin wasu mutane da yawa sun yi ikirarin cewa su ne shi, amma babu tabbas.

  • Amfanin Bitcoin: Bitcoin ya samu karbuwa a duniya kuma ya taimaka wa mutane da yawa wajen samun arziki. Wasu malaman addini sun halatta shi, wasu kuma sun haramta shi, amma mafi ingancin abin da za a ce shi ne, ciniki ne na siye da siyarwa.

  • Mining: Tun da aka fara Bitcoin, ana yin "mining" dinsa, wato hanyar samar da sabbin Bitcoin, wanda kuma har yanzu ana ci gaba da yi.

  • Sabbin Tsabar Kuɗi: A yanzu, akwai sabbin tsabar kuɗi da yawa da ake ƙirƙira a ƙarƙashin tsarin Bitcoin, kuma ana sa ran su ma su bunkasa kamar yadda Bitcoin ya yi. Misali shine Pi Network wanda shima ana yin "mining" dinsa a yanzu.




Menene Kasuwancin Kuɗin Dijital (Coin Trading)?

Coin trading na nufin siye da siyar da kuɗin dijital don samun riba daga hawa da saukar darajarsu. Darajar coin tana hawa daga misali N1.00 zuwa N1.03 ko sama da haka, ko kuma tana iya sauka daga N1.00 zuwa N0.93 dangane da yanayin kasuwa. Mutanen da suke siyan coin a lokacin da darajarsa ta yi ƙasa sannan su sayar a lokacin da ta yi sama don samun riba, ana kiran su 'yan ciniki (traders). Idan kuma sun rike coin ɗin na dogon lokaci, ana kiran su 'yan ajiya (holders).


Yadda Ake Samun Riba a Kasuwancin Kuɗin Dijital

Don samun riba mai yawa a kasuwancin coin, dole ne a samu jari mai yawa. Idan ba haka ba, riba za ta kasance ƙarama. Misali, idan ka saka jari har N10,000,000 a wani coin da darajarsa take N1.00, idan darajar ta haura zuwa N1.05 a cikin awa ɗaya, ribar ka zai zama N500,000 (N10,000,000 x 0.05). Idan kana da irin wannan jari, za ka iya samun riba mai yawa a kowace rana.

Yana da muhimmanci a san cewa kasuwancin coin ba shi da haɗari kamar Forex trading, sai dai idan ba ka da haƙuri, ko kuma ka buƙaci kuɗinka a lokacin da coin ɗin bai haura ba.


Hanyoyin Karanta Yanayin Kasuwar Coin

Don yin nasara a wannan kasuwanci, dole ne ka san yadda za ka karanta yanayin kasuwa. Ga wasu daga cikin muhimman tsare-tsare (patterns) da ake amfani da su wajen fahimtar yanayin kasuwa:

1. Tsare-Tsaren Canjin Yanayi (Reversal Patterns): Waɗannan tsare-tsaren suna nuna cewa yanayin kasuwar zai canza daga sama zuwa ƙasa ko akasin haka.

  • Double Top

  • Double Bottom

  • Head and Shoulders

  • Inverse Head and Shoulders

  • Rising Wedge

  • Falling Wedge

2. Tsare-Tsaren Ci Gaba (Continuation Patterns): Waɗannan tsare-tsaren suna nuna cewa yanayin kasuwar zai ci gaba da tafiya a hanyar da yake a kai.

  • Rising Wedge

  • Falling Wedge

  • Bullish Rectangle

  • Bearish Rectangle

3. Tsare-Tsaren Bangarori Biyu (Bilateral Patterns): Waɗannan tsare-tsaren suna nuna cewa kasuwa na iya tafiya zuwa sama ko zuwa ƙasa.

  • Ascending Triangle

  • Descending Triangle

  • Symmetrical Triangle

Baya ga waɗannan, akwai kuma Candlestick Patterns waɗanda su ma suke da mahimmanci ga 'yan ciniki na ɗan gajeren lokaci da kuma masu Forex trading.


Forex Trading da Makamantan sa

Forex trading yana da haɗari sosai. Saboda yadda yake da saurin samun riba mai yawa, haka kuma yana da saurin cin asara baki ɗaya. Saboda haka, dole ne a yi taka-tsantsan wajen mu'amala da shi. Amma duk da haka, ana iya amfani da wasu coins don yin irin Forex trading ɗin nan, wanda ake kira Futures Trading. Shima Futures Trading yana da matuƙar haɗari kamar Forex trading.

Don haka, duk wanda yake da sha'awar shiga Forex trading ko makamancinsa, dole ne ya nemi ilimi sosai. Idan ba haka ba, zai iya rasa dukiyarsa baki ɗaya.

👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇



 








Tags

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.

Top Post Ad

Below Post Ad